Labaran Wasanni
Za mu bunƙasa wasannin masu buƙata ta musamman -Sunday Dare
Biyo bayan ƙaddamar da wasannin masu buƙata , ta musamman karo na farko , mai taken ‘First maiden National Para Games Abuja 2022’ da akayi Asabar 09 ga Afrilu 2022, gwamnatin tarayya ta sha alwashin cigaba da ɗaukaka wasannin masu buƙata ta musamman (Nakasassu), a faɗin Najeriya.
Ministan matasa da wasanni Sunday Dare , ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai, bayan bude gasar a filin wasa na kasa na Moshood Abiola, dake birnin tarayya Abuja.
Sunday Dare, yace duk da ƙalubalen da aka samu na rashin kuɗaɗen gudanar da gasar , hakan bai sa sunyi ƙasa a gwiwa ba , duba da yadda aka ƙirƙiri sabon sashen wasannin masu buƙata ta musamman a watan Disambar shekarar 2021.
“Ya zama tilas muyi duk mai yiwuwa wajen ganin cewar an bunƙasa wasannin masu buƙata ta musamman a ƙasar nan”.
“A baya bayan nan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari , ya kafa sabuwar ma’aikata ta masu buƙata ta musamman , don haka lokaci yayi da kamfanoni zasu shigo a haɗa hannu da gwamnati don cigaba da bunƙasa wasannin a gaba , kuma tilas mu godewa Alhaji Aliko Dangote saboda gudunmowar da yake bawa wasanni” inji Sunday Dare.
Gasar wacce za a fara a Lahadi 10 ga Afrilu , jihohi 21 ne suka shiga gasar da kawo yanzu haka 17, daga ciki sun halarci sansanin da aka sauke su na Masu bautar ƙasa wato (NYSC), dake Kubwa a Abuja , kafin fara wasannin a filin wasa na Moshood Abiola.
Jihar Kano, na daga kan gaba a yawan ‘yan wasa da zasu wakilce ta a gasar , da zata fafata a wasanni daban -daban, har 10, da suka haɗa da , ƙwallon ƙafa ta Kurame (Deaf soccer ) sai ƙwallon masu ƙafa ɗaya (Amputee soccer ), da Taekwondo da Ƙwallon Tebur (Table Tennis ), da ninƙaya (Swimming).
You must be logged in to post a comment Login