Labaran Kano
zamu cigaba da bawa matasan ‘yan wasa fifiko -Bashir Mai Zare
Daraktan wasanni a hukumar wasanni ta jihar Kano, Bashir Ahmad Mai Zare, ya ce jihar Kano zata ci gaba da bawa matasa fifiko don bunkasa harkokin wasanni tun daga tushe.
Mai Zare, ya bayyana haka ne a zantawar sa da ‘yan Jaridu , a Jumma’a 3 ga Satumba 2021, a wasannin neman cancanta na shiga gasar wasannin matasa na kasa, shiyyar Arewa maso Yamma dake gudana a birnin Kebbi na jihar.
Daraktan ya ce kawo yanzu haka , jihar Kano ta shiga wasanni Biyar da ake fafatawa da ita , ciki har da tawaga uku da ta kunshi ta Maza da Mata, wato Zari Ruga (Rugby) Kwallon Kwando (Basketball), da kwallon Volleyball, sai Kwallon kafa da kuka Kwallon hannu ta (Hand Ball ).
“Tabbas akwai kalubale musamman ma na tsaikon da aka samu wajen zuwan jihohin Kaduna da Zamfara duba da tantancewar su data banbanta da sauran kungiyoyin da suka halarta daga farko”
“Haka zalika rashin fara wasannin akan Lokaci sakamakon tsaikon yasa zamu kara wasu kwanakin da shima wani Kalubale ne da bamuyi Shirin sa ba, amma hakan ba zai hana ‘yan wasan mu tasiri a wasanni ba” inji Mai Zare.
Kawo yanzu haka tawagar ta jihar Kano a Kebbi, na cigaba da samun nasarori a wasannin Kwallon Volleyball dana Zari Ruga, da ta samu galaba akan jihohi Kebbi da Sokoto, a wasan na matasa ‘yan kasa da shekaru 15, sama da 700, daga jihohi 7, da suka hada da, Kano, Katsina, Kebbi, Kaduna Jigawa, Sokoto da Zamfara, na shiyyar ke fafatawa a jihar ta Kebbi.
You must be logged in to post a comment Login