Labarai
Zamu fitar da tsare tsare masu dorewa a kwalejin Daura – Dr Aliyu Mamman
Shugaban kwalejin Fasaha da kere kere ta tarraya dake Daura a jihar Katsina Dakta Aliyu Mamman , ya tabbatar da cewar Kwalejin zata fito da tsare tsare da kyawawan manufofin wharkokin Ilimi dai dai dana zamani da zai bunkasa jihar da Najeriya da sauran kasashen duniya.
Dakta Aliyu Mamman, ya bayyana haka ne a Litinin 20 ga Disamba 2020, a wani taron kwana uku na kwararru da masu ruwa da tsaki da aka bude na tattaunawa da fitar da tsarin gudanar da sabuwar makarantar tare da cigaban ta na aiyyukan harkokin koyo da koyarwa.
Shugaban ya kara dacewa , muhimman abubuwa uku da suka hada da wasu tsare tsare da makarantar ta sa gaba da shigar da masana cikin harkar gudanarwa da samar da aiki ingantacce da za a barwa masu zuwa daga baya don dorawa a gaba na daga cikin abinda za a fi baiwa fifiko.
Dr Aliyu Mamman, yace haka zalika manufofin zasu zama wani damba na duba yanayin yadda fara gudanar da makarantar zai kasance a shekarar badi ta 2021.
Taron makalar tsare- tsare da aka fara wacce zata gudana tsawon kwana uku, ta samu halartar Dr Salisu Ladan da Dr Ibrahim Ahmad Idi sai Malam Falalu Ilayasu da Farfesa Murtala Sabo Sagagi.
You must be logged in to post a comment Login