Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zamu kafa kwamitin bibiyar yadda ake cunkusa yara a ajujuwan makarantu – Ganduje

Published

on

Gwamnatin Kano ta ce za ta dauki mataki mai tsauri a kan makarantun da ke cakuda dalibai da yawa a cikin azuzuwa.

A cewar gwamnatin ta lura da yadda ake cunkusa yara a ajujuwan makarantun wanda hakan karya doka ce ta yaki da cutar corona.

Babbar Sakatariya a ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano Hajiya Lauratu Ado Diso ce ta bayyana hakan ga manema labarai.

Ta ce, za’a fara bibiyar makarantun da basa kula da tsaftar muhallan su musamman bandakuna la’akari da yadda hakan ke zama barazana ga lafiyar dalibai.

Hajiya Lauratu ta kara cewa, gwamnati za ta kafa kwamati na musamman domin bibiyar makarantun dake karya ka’idojin lura da tsafta da kula saka dalibai da yawa a cikin aji tare da daukar matakai masu tsauri a kansu

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!