Kimiyya
Zamu kara adadin daliban da muke dauka a kwalejin lafiya – Dr Bello
Kwalejin horar da ma’aikatan lafiya ta jiha, wato School of Health Technology Kano , zata kara adadin yawan daliban da makarantar ke dauka daga dari 325, zuwa 700 don bunkasa ilimin da harkokin lafiya a jihar Kano.
Shugaban Kwalejin Dr Bello Dalhatu ne ya bayyana hakan a yau, lokacin da ya karbi tawagar tsoffin daliban Kwalejin horar da aikin lafiya ta dalibai Musulmai dake Funtua , wato Muslim a Community College of Health Science Funtua.
Dr Bello yanzu haka shi ke rikon mukamin shugaban tsofin daliban na Funtua, sun ziyarce shi yau a ofishin sa don taya shi murnar zama shugaban Kwalejin ta jihar Kano.
Dr Bello Dalhatu ya kara dacewa duk da kalubale da dama da ake fuskanta, hakan ba zai sa suyi kasa a gwiwa ba wajen kara yawan darasun koyar don samar da yawan dalibai da suka cancanta ‘yan asalin jiha da makwabta , sakamakon karancin da ake na ma’aikatan lafiya.
A nata jawabin,mataimakiyar shugaban tsoffin daliban kana Malama a Kwalejin koyar da aikin lafiya dake Daura, Aisha Bawa, ta yi karin bayani kan makusidin ziyarar tasu ga sabon shugaban.
Wakilinmu Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito mana cewa , tawagar ta karrama Dr Bello Dalhatu tare da bashi kyutar girmamawa a yayin ziyarar tasu.
You must be logged in to post a comment Login