Kiwon Lafiya
Zamu kawo cikas ga a jarrabawar Jamb, inji kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i da ke cikin yajin aiki
Kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i da ke cikin yajin akin a Jami’o’in kasar na sun yi barazanar kawo cikas a jarrabawar shiga manyan makarantu ta jamb ta wannan shekara da za ta gudana a ranar 9 ga watan Maris.
Shugaban hadakar kungiyoyin mista Samson Ugwoke ne ya yi barazanar yayin taron kungiyar na kasa da ya gudana a Abuja tsakanin shugabannin kungiyar na jihohi.
Sai dai ministan kwadago da samar da aikin yi sanata chris Ngige ya gudanar da wani kwarya-kwaryar taron sulhu tsakanin kungiyoyin inda ya bukaci kungiyar da su janye su kuma koma bakin aiki.
Ugwoke ya ce wannan barazana na da matukar muhimmanci, ganin yadda gwamnatin tarayya tayi shagulatun bangaro da dukkanin bukatun da suka mika mata.
In da ya ce tun da dai yajin aikin na su ya kai wannan mataki kungiyar ta yanke shawarar cewar da ga yanzu ba bu wani al’amari da za ci gaba da tafiya a dukkan jami’o’in kasar na.
Inda ya ce in dai mambobin su na yajin aiki kuma ana sa ran su taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da jarrabawar ta Jamb to hakan na nufin karya ka’idar ta.