Labarai
Zamu samar da sabuwar hanyar kama ‘yan kwaya – NDLEA
Shugaban hukumar NDLEA SP Ali Ado Kubau ya ce zasu kawo sababbin hanyar kama masu ta’ammali da kayayyakin maye da hodar ibilis a fadin jihar kano.
Ya bayyana hakan ne bayan kama wasu daga cikin irin wannan mutane masu ta’ammali da mugayen kwayoyin a unguwarnin da suka hada da Rimin Kebe da Hauren shanu da Jakara da Unguwar Yola da dai sauran su.
Hukumar NDLEA ta kama mutane 2 bisa zargin su da safarar miyagun kwayoyi
Hukumar NDLEA ta kama mutane 2 bisa zargin su da safarar miyagun kwayoyi
Hukumar NDLEA: Sun koka na yadda matasa ke ta’amali da kwayoyin Tramadol
SP Ali Ado ya kuma kara da cewa suna samun nasarar hakan ne ta dalilin sababbin hanyoyin da suke amfani da su wajen kama wadannan mutane a wuraren da suke zama suna shaye – shaye.