Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Zamu maye gurbin likitoci masu neman kwarewa da ‘yan bautar kasa – Minista

Published

on

Gwamnatin tarayya ta bai wa shugaban hukumar manyan asibitocin kasar nan umarnin da ta maye gurnbin likitocin da suka tsuduma yajin aiki da ‘yan hidimar kasa nan take.

Ministan lafiya Dr Osagie Ehanire ne ya bada umarnin ta cikin wata sanarwa da ya fitar da take mayar da martani akan yajin aikin da likitocin suka tsuduma.

Dakta Osagie ya ce kamata yayi likitocin suyi duba na tsanaki kan halin da kasar nan take ciki na matsin tattalin arziki kafin yanke hukunbcin tsuduma yajin aiki.

Sai dai ta cikin sanarwar ta bayyana cewa Gwamatin ta biya likitocin bukatun gudu Shida daga cikin guda Takwas.

A ranar Litinin din da ta gabata ne Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa suka tsuduma yajin aikin sai baba ta gani, sakamakon zargin da suka yiwa gwamnati na kin biya musu wasu daga cikin hakkokin su.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!