Labarai
Za mu tallafa wa Manoma a baɗi- SASAKAWA
Hukumar bunkasa harkokin noma ta Afrika watto Sassakawa da kuma shirin bunkasa noma da kiwo na jihar Kano watto KSADP ta bayyana cewa tallafa wa manoma da kayan Noma wata hanya ce da zata bunkasa harkokin noma a jihar Kano dama kasa baki daya.
Shugaban shirin a hukumar Sasakaawa a nan Kano Abdulrashid Hamisu Kofar mata ne ya bayyana haka yayi rabon kayan zazzabar shinkafa ga mata.
Abdulrashid Hamisu Kofarmata ya kuma ce sun shirya bada tallafin ga manoma maza da mata,a kokarin hukumar na nemo hanyoyin da za’a kawo karshen zaman banza a jihar kano, hakan yasa aka shirya gudanar da bada tallafin a kananan hukumomin kano baki daya.
A nasa bangaren mataimakin shugaban hukumar ta sasakawa na kasa Abdulrashid Gambo cewa yayi,burin hukumar shine ganin an fara sarrafa shinkafa mai inganci ta yadda zata yi gogayya da shinkafa yar waje
Da yake nasa jawabin shugaba hukumar Knarda a nan Kano Faruk Kurawa yabawa yayi da irin ayyukan hukumar ta sasakawa,
wasu mata da suka amfana da tallafin sun bayyana farin ciki game da tallafin da hukumar ta sasakwa ta basu na kayan zazzabar shinkafa
Shuwagabannin hukumar sun yi kira ga wadanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da kayan ta hanyar da ta dace domin bunkasa harkokin noma a fadin kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login