Labarai
Za muyi duk mai yiyuwa wajen inganta harka noma a Kano: SAA

Kungiyar dake kawo ci gaba akan harkokin noma a Afrika wato sasakawa ta bayyana cewa inganta harkar noma wata hanya ce da zata kawo cigaba mai dorewa a kasar nan.
Shugaban kungiyar na Kano Abdulrashid Kofar Mata ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da kungiyar ta fitar aka rabawa manema labarai.
Kofar Mata yace kungiyar ta dukufa wajen koyawa manoma sabbin dabarun aikin noma, domin samun wadataccen abinci a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login