Labarai
Zango ya mayar wa makafi martani
Makafi sun fusata kan yadda ake amfani da karin magana mai alaka da su, da wasu daga cikin ‘yan jaridu ke amfani da shi a kafafan yada labarai.
Wasu makafin dalibai dake karatu a makarantar masu bukata ta musamman dake tudun maliki a nan Kano, sun nuna rashin jin dadin su bisa yadda al’umma ke amfani da wasu karin magana da ke da alaka da su musamman yadda ‘yan jaridar wannan zamani ke yawan fadar su.
A zantawar Shugaban daliban Ibrahim Isma’il Abdullahi ya yi da wakilin Freedom Radio Salisu Baffayo, ya shaida masa cewa akwai wasu karin magana guda biyu da daya daga cikin masu gabatar da shirin Inda Ranka Nasiru Zangon yake amfani da su wajen gudanar da shirinsa irinsu Bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne, da Ba a rarrabewa da baccin makaho da Kar a haifi da marar ido da dai sauransu.
Haka kuma ya kara da cewa duk sanda ya ji an ambaci irin wadannan Karin Magana suna bata masa rai sosai don haka yake kira ga ‘yan jaridu da su daina amfani da kalmomin.
Shirin Inda Ranka na ranar 10/12/2019 tare da Yusuf Ali Abdallah
Masu bukata ta mussaman sun sami tallafi -Dr. Bunkure
Muna fuskantar kalubale – masu bukata ta musamman
Ibrahim Isma’il Abdullahi, ya kuma bukaci masu amfani da irin wadannan Karin Magana da su nemi wasu da zasu rika amfani da su, amma su kauracewa amfani da wadancan, domin tamkar cin fuska ne ga masu bukata ta musamman.
Sai dai da muka tuntubi Nasiru Salisu Zango kan korafin da makafin suka yi mai zai iya cewa, ya ce a gaskiyar lamari ba zai iya dena amfani da karin maganar ba kasancewar shima zuwa yayi ya tarar ana amfani da su, hasalima ba da su yake ba.
Ka zalika Zangon ya buga misali da karin maganar “Balbela da farin ta aka ganta’’ wanda akasari ana amfani da shi kuma ba yadda za’a sauya ta.
A cewar Zango zai dai duba yuwar rage amfani da karin maganar amma ba dai ya dena baki daya ba.