Labarai
Zargi: Ba mu zaftare albashin kowa a KAROTA ba – Baffa Babba
Hukumar KAROTA ta jihar Kano, ta musanta zargin zaftare albashin wasu daga cikin ma’aikatan ta, kamar yadda ake ta yaɗawa.
Shugaban hukumar Baffa Babba Danagundi ne ya bayyana hakan, yayin zantawar sa da Freedom Radio ta wayar tarho, a wani ɓangare na shirin Barka da Hantsi na Freedom Radio.
“Babu wani ma’aikaci da muka zaftare albashin sa, idan kuma kawai wanda yaga an zaftare masa to ya zo yayi ƙorafi a hukumar” a cewar Baffa.
Jami’in KAROTA ne ya haifar da hatsarin Kano Club – Ƴan Sanda
Da yake bayani kan zargin korar ma’aikata a hukumar KAROTA, Baffa ya ce “mafi yawa daga ma’aikatan da muka kora, mun same su da laifin ƙin zuwa aiki, yayin da wasu kuma muka kama su da laifin karɓar albashin waɗanda suka rasu”.
Baffa Babba ya kuma ce duk wanda yaga an cire kuɗin sa, to ba daga hukumar ba ne, daga hukumar kula da ma’aikata ne.
You must be logged in to post a comment Login