Labarai
Zargin badakala: Majalisar wakilai ta yi barazanar kama shugabannin kamfanin NNPC
Majalisar wakilai ta bai wa wasu hukumomi goma sha bakwai da ke karkashin kamfanin mai na kasa (NNPC) wa’adin mako guda da su gurfana gaban kwamitinta da ke kula da asusun gwamnati don tattauna wasu al’amura da suka shige duhu ga ‘yan majalisar.
A cewar majalisar gaza bayyanan jami’an gaban kwamitin zai sanya taga ba ta da zabi da ya wuce ta ba da umarnin kama shugabannin hukumomin don gurfanar da su.
A kwanakin baya ne dai ofishin babban mai binciken kudi na tarayya ya aika da takardar tuhuma ga hukumomin sakamakon gaza fayyace kididdigar yadda suka sarrafa kudadensu na tsawon shekaru.
Wasu daga cikin hukumomin sun hada da: hukumar bunkasa bangaren man fetur ta kasa da kamfanin tallata man fetur da kuma hukumar kayyade farashin man fetur.
You must be logged in to post a comment Login