Labarai
Zargin rashawa: An fara mayar wa da malamai kuɗin addu’ar da aka zaftare musu
Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta Kano ta ce, tuni waɗanda ake zargi da zaftarewa malamai kuɗin addu’a suka fara mayar da kuɗin ga waɗanda suka karɓarwa, ta hannun hukumar bayan da ta ƙaddamar da bincike a kai.
Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado ya shaidawa Freedom Radio cewa, binciken su ya tabbatar da zarge-zargen da aka yiwa mai baiwa gwamnan Kano shawara kan addinai da ɗansa da kuma wasu mutane, na zaftarewa malamai kuɗin addu’ar da gwamna ya basu.
A cewar Muhyi yanzu haka sun mayarwa da mutane bakwai kuɗaɗensu sannan suna ci gaba da faɗaɗa bincike a kai tare da tattara ƙarin hujjoji domin gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.
Ya ƙara da cewa, abin da mai baiwa gwamnan shawara da waɗannan mutane suka aikata na wabcewa malaman kuɗin addu’a ya saɓa da doka, kuma a yanzu sun samu gamsassun dalilai waɗanda suka tabbatar da hakan.
You must be logged in to post a comment Login