Labarai
Zulum- ya baiwa malamai 30 kwangilar addu’o’i a kasa mai tsarki
Gwamnatin jihar Borno ta umarci manyan malamai guda talatin da su gudanar da addu’oin kan kungiyar mayakan Boko Haram da suka jima suna kawo tashe-tashen hankula a jihar.
Gwamnan jihar ta Borno Babagana Zulum ne ya bukaci hakan ta cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun gwamnan Isa Gusau ya fitar ga manema labarai.
Sanarwar ta kuma ce gwamnan ya lashi takobin baiwa malaman guda talatin zuwa a kasar Saudi Arebiya da su gudanar da addu’oin kan rikicin na mayakan na Boko haram da ya dauki shekaru yana gudana a jihar.
Isa Gusau ta cikin sanarwar ya kuma ce gwamnan jihar ta Borno ya kuma umarci malaman dake zaune a kasar saudiyya da su dinga gudanar da dawafi a kowacce rana a ka’aba dan samun cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ta Borno dama kasar nan baki daya.
Ya kuma ce malamai talatin din dna zaune a kasar Saudiyya da suka fito daga jihohin Borno da Katsina da Zamfara da kuma nan jihar Kano dama wasu sassan jihohin dake yankin Arewacin kasar nan.
Ya kuma ce malaman za su kasance ne a koda yaushe a bakin ka’aba suna rokawa jihar ta Borno da kasar nan zaman lafiya da kwanciyar hankali.