Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zuwa yanzu mun rufe layukan waya sama da Miliyan 72 – NCC

Published

on

Hukumar Sadarwa ta kasa NCC tace zuwa yanzu ta rufe layukan sadarwa da ba’a hada da lambar shaidar zama dan kasa ba sama da miliyan 72.

Jami’i a hukumar mai kula da shiyyar arewa maso yamma da arewa maso kudu Alhaji Shu’aibu Suwade ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.

“Mun kulle layukan waya sama da miliyan 72 domin an dade ana fadawa mutane su hada lambar wayarsu da lambar shaidar zama dan kasa kafin wannan mataki.”

“Sau hudu ana dage ranar da za’a fara rufe layukan da ba’a hada da NIN ba saboda haka duk wanda aka rufewa layi shi ne ya jawa kansa”

Suwade ya kuma ce duk wadanda aka rufewa layukan zasu iya ziyartar kamfanin sadarwa mafi kusa don a bude layin ko kuma masu amfani da Layin MTN su danna *785*NIN# masu Aitel kuma su danna *121*1*NIN#

9Mobile kuma *200*8#.

A makon da muke ciki ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin dakatar da duk wani layin da ba a hade shi da lambar NIN ba, wanda ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani Farfesa Isah Isa Ibrahim Fantami ya sanar da hakan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!