Labarai
Ƙudurin samar da masarautu masu daraja ta biyu a Kano ya tsallake karatu na ɗaya
Ƙudurin dokar samar da masarautu masu Daraja ta biyu a Kano, ya tsallake karatu na ɗaya a zauren majalisar dokokin jihar Kano.
Ƙudurin ya kai wannan mataki ne yayin zama na musamman da majalisar ta yi yau Juma’a bayan da magatakardan majalisar Alhaji Bashir Idris Diso ya gabatar da karatun dokar wanda kuma ya samu sahalewar mambobin zauren.
You must be logged in to post a comment Login