Connect with us

Labarai

Ƴan bindiga sun harbe magidanci har lahira a Kano

Published

on

Wasu ƴan bindiga sun harbe wani magidanci Ahmad Sani Abbas mai kimanin shekaru 30 har lahira a Kano.

Ɗan uwan marigayin Kamal Sani Abbas ya shaida wa Freedom Radio cewa, al’amarin ya faru ne a daren ranar Jumu’a, bayan ƙarfe 9 na dare a yankin Gezawa, lokacin da yake hanyar sa ta zuwa sada zumunta.

A nan ne ƴan bindigar suka tare shi tare da buɗe masa wuta, lamarin da yayi sanadiyyar rasa ran sa.

Kamal ya ce, ƴan sandan Gezawa ne suka kawo musu gawar marigayin, amma ba su yi musu ƙarin bayani ba.

Karin labarai:

‘Ƴan bindiga sun hallaka mutane biyu a Kano

Rashin Tsaro: Ƴan bindiga sun sace mahaifiyar wani attajiri tare da ajalin mutum guda a Kano

Marigayin ɗan uwa ne ga tsohon Kantoman ƙaramar hukumar Gwale Alhaji Abbas Sani Abbas, ya kuma rasu ya bar mace ɗaya da ‘ya guda ɗaya.

An yi jana’izar marigayin da misalin ƙarfe 12 na rana, inda aka binne shi a maƙabaratar Ɗandolo.

Mun yi ƙoƙari domin jin ta bakin rundunar ƴan sandan jihar Kano amma abin ya ci tura, kasancewar mai magana da yawun ƴan sandan DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa bai ɗauki kiraye-kirayen wayar da muka yi masa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!