Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan sanda sun cafke masu bai wa yan ta’adda mafaka

Published

on

Rundunar ‘yan Jihar Jigawa ta ce, ta samu nasarar kama wasu mutane biyu da ake zarginsu da laifin hada kai da kuma bai wa wasu masu garkuwa da mutane mafaka da kuma aikata laifin fashi da makami da sauran batagari.

Hakan na kunshe ne ya cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ASP Abubakar Isah ya fitar a daren yau Litinin.

Ta cikin sanarwar, ya ce, baya ga wadannan mutane da rundunar ta cafke, ta kuma kama wasu masu kwacen wayoyin mutane da sauran masu aikata laifi a jihar.

Haka kuma, ya ƙara da cewa, rundunar yan sandan ta jihar Jigawa, za ta ci gaba da fadada ayyukanta zuwa lungu da sako jihar, musamman a wannan lokaci na sanyi domin dakile duk wata barazanar rashin tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!