Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 5 a harin Rabah

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, ta tabbatar da mutuwar mutane biyar tare da kona kayan abinci da abubuwan hawa, a wani hari da ‘yan bindiga suka kai da safiyar Litinin din makon nan a garin Gidan Buwai da ke karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto.

Mai magana da yawun rundunar a jihar  ASP Ahmad Rufa’i, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da manema labarai.

Jami’in ya ce ‘yan bindigar sun shiga garin ne inda suka harbe mutane biyar, da kuma kona kayan abinci da babura da motoci, kafin daga baya jami’an tsaro na hadin gwiwa su kai dauki yankin.

A baya dai an samu makamancin wannan hari a garin Duhuwa na karamar hukumar Wurno da ke kusa da Rabah duk a jihar ta Sokoto da ya yi sanadiyyar salwantar rayukan mutane da dama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!