Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ɗaurin Aure: Hatsarin mota ya hallaka ƴan Kano 8 a hanyar Zariya

Published

on

Wasu matasa ƴan asalin jihar Kano takwas sun rasa ransu, sakamakon wani haɗarin mota.

Haɗarin ya faru ne yayin da suke hanyar dawowa daga ɗaurin aure da suka je garin Zariya, da yammacin ranar Asabar.

Waɗanda lamarin ya rutsa da su ƴan asalin unguwar Sani Mainagge ne da ke ƙaramar hukumar Gwale.

Ɗan uwan angon Abubakar Yusuf Usman ya shaida wa Freedom Radio cewa, an kawo gawar matasan 8.

Sannan ya ce, akwai ƙarin mutane 3 da suka rasa ransu sanadiyyar hatsarin, amma ba ƴan Kano ba ne.

Wakilin mu Aminu Abdu Baka Noma, ya raiwaito cewa, al’ummar unguwar Sani Mainaggen suka shiga cikin jimami.

Sannan an fara shirin yi musu jana’iza a gobe Lahadi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!