Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƙasar Saudiyya ta dakatar da amfani da dokokin yaƙi da cutar Corona

Published

on

Ƙasar Saudi Arabiya ta amince da dakatar da duk wasu takunkuman da ta sanya domin yaƙi da cutar corona.

A ranar Asabar ƙasar ta amince da daina sanya takunkumin rufe baki da hanci da kuma bada tazara tsakanin juna.

Matakin dai zai kawo ƙarshen bada tazara tsakanin masallata a cikin Masallatan Harami guda biyu da duk masallatan da ke cikin ƙasar.

Sai dai masallatan za su iya ci gaba da sanya takunkumin rufe baki da hanci idan suna da buƙatar hakan, ba tare da an tilasta musu ba kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta rawaito.

wadannan sabbin matakan za su fara aiki ne daga yau Asabar 5 ga watan Maris na 2022 kamar yadda wata majiya mai tushe a ma’aikatar harkokin cikin gidan ƙasar ta sanar.

Haka zalika, ƙasar ba za ta ƙara buƙatar kebance matafiya ba don tabbatar da basa ɗauke da cutar COVID-19, ko kuma nuna shaidar takardar yin gwajin cutar ta PCR ba bayan saukar su a ƙasar ta Saudiyya.

Ƙasar ta kuma ɗage dakatarwar da ta yi na zirga-zirgar jiragen sama dake shiga ƙasar daga ƙasashen Afirka ta Kudu, Namibia, Botswana, Zimbabwe, Lesotho, Eswatini, Mozambique, Malawi, Mauritius, Zambia, Madagascar, Angola, Seychelles, Comoros, Nigeria, Ethiopia, da kuma Afghanistan.

Majiyar ta kuma bayyana cewa matakan da aka ɗauka sun biyo bayan ci gaba da aka samu a yaki da cutar corona kuma za a ci gaba da tattaunawa da ƙwararrun hukumomin kiwon lafiya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!