Labarai
Ƙungiyar likitoci ta NARD ta janye yajin aikin da ta ke yi

Ƙungiyar Likitocin masu neman ƙwarewa ta Najeriya NARD, ta sanar da dakatar da yajin aikin da ta fara na tsawon makonni hudu, bayan tattaunawa da Gwamnatin Tarayya da sanya hannu bisa yarjejeniyar fahimtar Juna.
Shugaban ƙungiyar ta NARD, Dakta Mohammad Suleiman, ya bayyana wannan mataki a matsayin bawa gwamnati damar aiwatar da abubuwan da har yanzu ba a warware ba daga cikin bukatun ƙungiyar.
Daga cikin muhimman abubuwan da kungiyar ke bukata daga wajen gwamnati akwai biyan bashin karin albashi da sauran bashin baya-bayan nan, aiwatar da karin albashi da inganta tsarin aikin likitoci.
Dakta Suleiman ya gargadi ‘yan ƙungiyar cewa idan ba a cika dukkan abubuwan da ake jira ba cikin wa’adin makonni hudu, NARD za ta koma yajin aiki na din-din-din.
You must be logged in to post a comment Login