Addini
Ƴan bindiga sun kashe sama da mutane 100 a Burkina Faso

Ƴan bindiga sun kashe mutane sama da ɗari a ƙasar Burkina Faso.
Rahotanni sun ce ƴan bindigar sun kashe mutanen ne a wani ƙauye da ke arewacin ƙasar.
A cewar hukumomi a birnin Qagadougou wannan shine hari mafi muni da aka kai kasar a ƴan shekarun nan.
Shaidun gani da ido sun shaidawa manema labarai cewa, ƴan bindigar sun kashe mutanen ne a daren jiya juma’a a kauyne Solhan da ke l;ardin Yagha daf da kan iyakar ƙasar da jamhuriyar Nija, a cewar mai magana da yawun gwamnatin ƙasar Ousseni Tamboura
You must be logged in to post a comment Login