Labarai
Ƴan sanda sun musanta yin kisan kai a Kano
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta musanta zargin cewa jami’anta sun hallaka wani matashi Saifullahi Abdullahi mai shekaru 23 a unguwar Ƙofar Mata da ke ƙaramar hukumar Birni.
Mai magana da yawun ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa cikin wani saƙon murya da ya aike wa Freedom Radio ya ce, tun farko sun samu rahoton ɓarkewar fadan daba ne a unguwar Ƙofar Mata da ƙarfe 1 da mintuna 40 na dare.
Ya ce, “Ƴan sanda sun halarci wurin tare da kama mutane biyu suka sanya musu ankwa, sannan suka bar su tare da ɗan sanda guda ɗaya a mota, suka bazama cikin unguwar domin faɗaɗa bincike, sai dai kafin su dawo wasu da ake zargin ƴan daba ne suka dawo inda motar ta ke suka kuɓutar da waɗanda aka cafke, sannan suka yiwa ɗan sandan da aka bari rauni tare da wani mutum guda.”
Ƴan sanda sun garzaya da ɗan sandan da aka yiwa rauni da kuma mutum ɗaya mai suna Saifullahi Abdullahi zuwa asibiti wanda a nan ne kuma rai ya yi halinsa a cewarsa.
Ƙarin labarai
Jami’an tsaro sun gayyaci masu shirya zanga-zanga a Kano
#EndSARS : Buhari ya gargadi masu zanga-zanga
Mazauna unguwar dai sun zargi ƴan sandan da hallaka matashin inda har suka gudanar da zanga-zanga wadda ta kai ga lalata motar ƴan sanda guda ɗaya.
You must be logged in to post a comment Login