Labarai
Ƴan sandan Kano sun cafke mutumin da ya banka wuta a Masallaci
Ƴan sanda a jihar Kano sun cafke wani mutum mai suna Shafi’u Abubakar mai shekaru 38 bisa zarginsa da banka wuta a Masallaci yayin da ake tsaka da yin Sallar Asuba.
Rahotonni sun bayyana cewa, mutane sama da 20 ne suka jikkata ciki har da shi mai kunna wutar.
Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa, binciken farko da ta gudanar ta gano cewa mutumin ya banka wutar ne biyo bayan rikicin gado da suke yi na shi da ƴan uwansa.
Sai dai daga bisani limamin Masallacin tare da ƙarin mutum biyu sun rasu a asibitin ƙwararru na Murtala.
You must be logged in to post a comment Login