Labarai
Ƴan ta’adda dubu 8 ne suka zubar da makaman yaƙin su – Rundunar Soji

Babban kwamandan runduna ta bakwai mai yaƙi da ayyukan ta’addanci a ƙasar nan Birgediya Janar Abdulwahab Eyitayo, ya ce zuwa yanzu ƴan bindiga dubu 8 ne suka zubar da makaman su.
Birgediya Janar Abdulwahab Eyitayo ya bayyana hakan lokacin da ya karɓi baƙuncin mai magana da yawun rundunar sojin ƙasar nan Birgediya Janar Onyema Nwachukwu a Maiduguri.
Rundunar sojojin sama ta hallaka kwamandodin ‘yanbindiga biyar a Zamfara
Eyitayo ya ce, ƴan bindigan da ke boye a dajin Sambisa tuni sun watsar da makaman su tare da miƙa wuya ga sojoji.
Sai dai ya alaƙanta nasarar da yadda sojoji suka buɗe wuta a sassan da ake fuskantar matsalar tsaro, dalilin kenan da ƴan bindigar ke bayyana kan su da iyalan su.
You must be logged in to post a comment Login