Coronavirus
Ɓullar cutar Corona ta bunƙasa harkokin lafiya a Najeriya – Farfesa Isah
Sashin kula da cututtuka masu yaɗuwa a Asibitin Aminu Kano ta ce cutar corona ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu 3 a Nijeriya ciki har da likitoci da dama.
Haka kuma, cutar ta tilastawa wasu likitocin barin aikinsu.
Shugaban sashin Farfesa Isah Abubakar Sadiq ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da Freedom Radio, kan yadda Najeriya ta cika shekara biyu da samun rahoton ɓullar cutar Corona.
Farfesa Isah Abubakar ya kuma ce “cikin shekaru biyu da cutur ta haifar da talauci a tsakanin al’umma, Sannan ta tayi ajalin mutanen da dama da suke ɗauke da wasu cututtukan da ne saurin yin kisa.
“Ƙasashen duniya ba su taba fuskantar matsala a fannin lafiya da ilimi ba sai da cutar korona ta zo, sannan an samu koma baya a ɓangaren tattalin arziƙi da tafiye-tafiye kuma ta saka tsoro da firgici a tsakanin mutane”.
Da yake bayyana cigaban da aka samu dalilin cutar Farfesan ya ce ” Ɓullar cutar corona ta sanya an fito da sababbin dabaru na samar da magunguna da alluran rigakafi da kuma Kayan gwaje-gwaje, Sannan ta ɓunkasa fasahar sadarwa da kuma baiwa likitoci dabarun duba mara lafiya a zamanance”.
Sai dai ya shawarci mutane da su ci gaba da yin biyayya ga dokokin cutar don taƙaita yaɗuwar ta.
You must be logged in to post a comment Login