Manyan Labarai
Dawo da kadarorin sata abu ne mai wuya-Inji masanin tattalin arziki
Wani malami a sashin nazarin harkokin tattalin arziki dake jami’ar Bayero ta nan Kano Dakta Muhammad Sani Shehu, ya ce babban abu ne a ce a yanzu za a dawo da dukkan kadarorin kasar nan da ake zargin wasu jami’an gwamnati da sacewa da boyewa a wasu kasashen waje.
Malamin ya bayyana hakan ne ta cikin shirin “Barka da Hantsi” na nan tashar Freedom Rediyo, inda shirin ya mayar da hankali kan kafa kwamitin da zai rika bincikar ma’aikatan gwamnatin da suka mallaki kadarorin ta hanyar haram a gida Najeriya da kasashen waje.
Ya kara da cewa akwai matakan da al’umma za su bi wajen ganin an magance dukkan matsalolin da ake fama da su na tabarbarewar tattalin arziki kasar nan.
Wani lauya mai zaman kansa a nan Kano Barrister Abba Hikima, yace da al’umma za su kaucewa duk wani nau’i na cin hanci da rashawa a cikin harkokinsu, da kuwa sun cimma burin da ake zato na kwato dukkannin kayayyakin da aka wawure na kasar nan.
Bakin dai sun karkare da kira ga al’umma a kan su mayar da hankali wajen kwato ‘‘yancinsu domin kuwa har yanzu shi ne babban abinda ke damun ‘yan Najeriya.