Connect with us

Labarai

Covid-19: Najeriya za ta iya samun durkushewar tattalin arziki

Published

on

Shararren Malami akan zamantakewar al’umma na jamiar Bayero ta  Kano Farfesa Sani Lawan ya ce annobar  corona za ta haifar da matsalar durkushewar tattalin arzikin kasar nan da ma wasu kasashen sakamakon dukkanin wasu hada hada da ake gudanarwa sun tsaya sanadiyyar wannan cutar.

Farfesa sani lawan manumfashi ne ya bayyana hakan jim kadan bayana kammala shirin barka da hantsi na nan freedom radiyo da ya gudana da safiyar yau laraba wanda ya mai da hankali wajan tattaunawa kan hanyoyin da ya kamata al’ummah su dauka dan ganin an kare kai daga wannan cutar.

Sani Lawan Manumfashi ya kara da cewar wannan matakin da gwamnati ta dauka na takaita cakuduwa a tsakanin al’umma, dan kare kai daga wannan cutar,amma yana da kyau gwamnatin ta yi wani abu wajan ganin an fito da wani tsarin da talaka zai samu wani abu duba da cewar wannan mataki zai shafi rayuwar sa ta yau da kullum.

Farfesan ya kuma kara da cewar ya kamata hukumomi su sanya idanu akan mutane masu sana’ar jari bola duba da cewar bola na tattare da dukkanin wasu kwayoyin cututuka da ke yaduwa a tsakanin al’umma.

Sani Lawan Manumfashi ya kuma bukace gwamnati da ta kasance tana shirya wasu shirye-shirye dan kara wayar da kan al’umma game da wannan cutar dan kai daga fuskantar barazanar cutar a jihar nan.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,260 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!