Labarai
Ana samun karuwar shigo da magunguna daga kasashen waje – Kungiya
Kungiyar masu harhada magunguna ta kasa ta ce an samu karuwar shigo da magunguna zauwa Najeriya daga kasashen China da India da kudin su ya kai sama da biliyan biyu a wannan shekarar.
Shugaban kungiyar ta kasa Dr Anthony Ikeme ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Ya ce, kamata ya yi gwamnatin tarayya ta bunkasa masana’antun hada magunguna na kasar nan domin rage yawan kudin da ake fitarwa wajan sayan magunguna a sauran kasashe.
Dr Anthony ya kara da cewa har yanzu gwamnatin na bin kungiyoyi masu shigo da magunguna kasar nan bashin naira miliyan arba’in da daya da har yanzu basu biyata ba.
A don haka ya bukacin gwamnatin da ta mayar da hankali wajen inganta masana’antun sarrrafa magunguna na kasar nan, ta yadda za su rika samar da ingantattun magunguna da kuma rage yawan kudin da ake kashewa wajan sayo magani a wasu kasashen a kowacce shekara.
You must be logged in to post a comment Login