Labarai
Ƴan Shayi sun shiga halin matsin rayuwa a Kano
A watan Nuwamban shekarar 2020 da ta gabata, hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS ta ce, tattalin arziƙin Najeriya ya samu koma-baya da kashi 3.65 a tsakanin watan Yuli zuwa Satumba, wanda hakan ke nufin ƙasar na samun ci-baya.
To a nan Kano dai halin matsin rayuwar na ci gaba da shafar rukunin al’umma.
Wani bincike da Freedom Radio ta yi, ya gano cewa da dama yaran da ake yiwa Shayi a yanzu sun faɗa cikin halin matsin tattalin arziƙin.
Me ya jefa ƴan shayi cikin matsin rayuwa?
Bisa al’adar Malam Bahaushe, ƴan uwa da abokan arziƙi kan gwangwaje ɗan Kaciya da tallafin Kaji da kayan ƙwalam da maƙwalashe wasu lokutan ma har da sabbin ɗinkuna kala-kala, kamar yadda wata dattijuwa da ta ga jiya ta ga yau ta shaida wa Freedom Radio.
Karin labarai:
Cin zarafin mata yana karuwa a Najeriya
Mun kama Sarkin mayu na bogi-Muhiyi Magaji
To amma iyaye a yanzu sun ce lamarin sauya, domin idan an yiwa ƴaƴa Kaciya ana barinsu ne daga su sai makusantan su.
Malama Sumayya Nafi’u wata uwa ce da a yanzu take jiyyar ɗanta da aka yiwa shayi.
Ta ce, “Da manyan unguwa ne su ke ɗiban yara su kai su shayi, sannan su haɗo su da goma ta arziƙi”.
Ta ci gaba da cewa “Yanzu abin ya sauya kai zaka kai ɗan ka kuma in kun dawo daga ku sai makusantanku, babu mai tallafa muku saɓanin yadda ake a baya”.
Wanzamai dai su ne ke yin shayi a ƙasar Hausa, hakan ya sa muka ziyarci fadar Sarkin Askar Kano Malam Muhammad Yunusa Nabango.
Sarkin Askar ya ce, juyi-juya halin zamani ne ya gamu da batun aikinsu na shayi.
Me Sarkin Aska ya ke ji daga wurin iyayen ƴan Shayi?
Sarkin Askar ya ce, batun gaskiya yanzu ba a kai wa ƴan Shayi, kaɓakin da aka saba yi musu a zamanin baya.
Ya ce, “La’akari da rahotannin da nake samu daga iyaye, na nuna cewa yanzu babu taimakekeniyar a yi maka hidima don an yiwa ɗanka Shayi”.
Waɗanne hanyoyi za a bi domin farfaɗo da wannan al’ada ta taimakekeniya tsakanin juna?
Sarkin Askar ya ce, Al’ummar su yi riƙo da al’adun domin su ne abin da addini ya koyar da su, ba birgewa ba ce ajiye waɗannan al’adun.
Shin ku ya ya abin ya ke a yankunan ku?
You must be logged in to post a comment Login