Labarai
Muhallai sama da miliyan biyu ne suka salwanta a Nijeriya damunar bana: NEMA
- Mutane samada miliyan biyu da dubu dari hudu ne suka rasa muhallansu a Najeriya sakamakom ambaliyar ruwa.
- An bayyana hakan ne lokacin buɗe taron mako guda na masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a Abuja.
- Taron mako gudan na masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya ya zo dai-dai da lokacin da kasar nan ke farfadowa daga barnar ambaliyar ruwan daya auku.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA Mustapha Ahmed ya ce mutum miliyan biyu da dubu dari hudu ne suka rasa muhallansu sakamakon matsalar ambaliyar ruwan da aka fuskanta a gurare daban-daban a daminar gabata.
Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne jiya Litinin a Abuja lokacin buɗe taron mako guda na masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya.
Mustapha Ahmed ya ce taron wanda zai horar da jami’an hukumar game da ayyukansu an shirya shi ne a daidai lokacin da kasar nan ke farfadowa daga barnar da ambaliyar ruwar ta haddasa.
Ya kara da cewa mutane 662 ne suka rasa rayukansu, wasu kimanin 3,174 suka samu raunuka, sai kuma miliyan 2, 430, 445 da suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar.
Ranoton: Abdulkadir Yusuf Gwarzo
You must be logged in to post a comment Login