Labarai
Ma’aikatan INEC na wucin gadi sun yi barazanar kin fita aiki bisa rashin biyan alawus
Ma’aikatan wucin gadi na hukumar zabe ta INEC da suka yi aikin zaben shugaban kasa da yan majalisar tarayya a karamar hukumar Nassarawa da ke jihar Kano, sun yi barazanar kaurace wa aikin zaben gwamnoni da yan majalisar jiha a gobe Asabar sakamakon rashin biyan hakkokin sun a zaben na baya.
Da suke zantawa da wakiliayr Freedom Radio Hafsat Ibrahim Kawo, ma’aikatan na wucin gadi, sun bayyana cewa, hukumar zabe mai zaman kanta INEC, ba ta biya su kudaden alawus na horon da suka yi ba na zaben shugaban kasa da aka gudanar tun a ranar 25 ga watan jiya na Faburairu.
Haka kuma sun bukaci mahukuntan da abun ya shafa da su yi diuk mai yiwuwa wajen ganin cewa hakkin nasu ya fiya.
Masu korafin sun kara da cewa, sun cike duk wasu takardu da aka bukata domin biyan kudin nasu, sai dai har kawo yanzu da ya rage sa’o’i kadan a fara kada kuri’ar gwamnoni da yan majalisar jihohi hakkin nasu na baya ya makale.
Ma’aikatan INEC din na wucin gadi na karamar hukumar Nassarawa, sun kara da cewa ba za su yi aikin na gobe ba matukar hakkokin nasu ba su fita ba.
Rahoton: Hafsat Ibrahim Kawo
You must be logged in to post a comment Login