Labaran Kano
Gwamna Abba Kabir ya aika wa majalisa sunayen sabbin Kwamishinoni

Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya aike wa majalisar dokoki sunayen mutane 19 domin tantancewa tare da amincewar naɗa su a matsayin Kwamishinoni.
Gwamnan ya buƙaci tantancewar tasu ne ta cikin wata wasiƙa da ya aike majalisar wadda shugabanta Jibril Isma’il Falgore ya karanta ta a zaman majalisar na yau Talata.
Waɗannan gwamnan ya aika da sunayen nasu sun hada da:
1- Comrade Aminu Abdulsalam
2- Hon. Umar Doguwa
3- Hon. Ali Haruna Makoda
4- Hon. Abubakar Labaran Yusuf
5- Hon. Danjuma Mahmoud
6- Hon. Musa Shanono
7- Hon. Abbas Sani Abbas
8- Haj. Aisha Saji
9- Haj. Ladidi Garko
10- Dr. Marwan Ahmad
11- Engr. Muhd Diggol
12- Hon. Adamu Aliyu Kibiya
13- Dr. Yusuf Kofar Mata
14- Hon. Hamza Safiyanu
15- Hon. Tajo Usman Zaura
16- Sheikh Tijjani Auwal
17- Hon. Nasiru Sule Garo
18- Hon. Haruna Isa Dederi
19- Hon. Baba Halilu Dantiye
Majalisar dokokin, ta sanya gobe Laraba da misalin ƙarfe 10:00 na safe a matsayin lokacin da za ta tantance waɗanda gwamnan ya aike da sunayen nasu.
You must be logged in to post a comment Login