Labarai
NEMA ta karbi yan Nijeriya 146 da suka makale a Yamai
Hukumar ba da Agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA ta karbi ‘yan kasar 146 da suka makale a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, dake kan hanyarsu ta zuwa kasashen ketare da nufin neman arziki.
Shugaban hukumar shiyar Kano Dakta Nura Abdullahi ne ya bayyana haka a jiya Alhamis yayin zantawarsa da Freedom radiyo.
Dakta Abdullahi ya ce ‘wadanda aka kamo ‘yan asalin kasar sun dawo ne ta hanyar wani shiri na mayar da ‘yan gudun hijira gida, karkashin kulawar hukumar kula da ‘yan cirani ta duniya IOM’.
Wadanda aka dawo da su sun hada da maza 56, da mata 39, sai yara 51 da suka hadar a mata 35 da maza 16 daga jihohin Katsina, Kano, Adamawa, Lagos, Imo, Enugu, Edo, da dai sauransu.
Rahoton: Ahmad Kabo Idris
You must be logged in to post a comment Login