Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Ƙetare

UN ta jaddada kudirinta na kawo karshen cutar HIV a 2030

Published

on

Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada cewa ‘za ta cimma kudirinta na kawo ƙarshen yaɗuwar cutar HIV zuwa shekarar 2030’.

Sai dai ta yi gargaɗin cewa ‘rashin kuɗin aiki da kuma nuna tsangwama ga masu cutar yana kawo cikas ga aikin’.

Kididdigar da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ta nuna cewa ‘mutum miliyan 39 ne ke ɗauke da cutar HIV a duniya’.

Kuma ‘akalla mutum miliyan 30 daga cikinsu ne ke karɓar maganin da ke rage kaifin cutar’.

Majalisar Dinkin Duniyar ta kuma ‘ce akwai buƙatar samun ƙarin kuɗin yaƙi da cutar, da kuma mayar da hankali daga bangaren gwamnatoci, idan har ana son kawar da ita’.

Rahoton: Ahmad Kabo Idris

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!