Labarai
Karota ta kama matasa da buga takaddun bogi a Kano
Hukumar kula da zirga zirgar Ababen Hawa ta Kano (KAROTA) ta samu nasarar kama wasu matasa masu buga takaddun bogi tare da siyarwa Direbobi masu daukar kaya (Way Bill) a wasu sassan titunan jihar Kano.
Shugaban Hukumar KAROTA Injiniya Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana hakan ta bakin Kakakin Hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa.
Hukumar ta ce yanzu haka matasan sun shiga hannunta, idan kuma sun kammala bincike za su mika su ga Jami’an ‘Yansandan domin fadada bincike tare da daukar Matakin da ya dace
Hukumar ta cigaba da cewa a baya an sha samun Korafe-korafe makamanta wannan sai yanzu Allah ya ba su nasarar Cafke wadanda ke buga way bill din na bogi tare da siyarwa da direbobi.
Karota ta ja hankalin Direbobi da su kula sosai don kaucewa fadawa hannun bata gari masu wannan mummunar ta’ada, ta kuma sha alwashin cewar ba za su bar duk wanda ke ƙokarin yi wa Hukumar zagon ƙasa a ayyukanta ba a fadin Jihar.
Rahoton: Abubakar Tijjani Rabi’u
You must be logged in to post a comment Login