Labarai
Majalisar tattalin arziki tayi Kira ga NEMA ta gaggauta raba kayan abincin a Nijeriya
Majalisar tattalin arziki ta kasa da yi Kira ga hukumar bada again gaggawar ta Nijeriya NEMA da ta gaggauta fitar da kayan hatsi zuwa garuruwa, don ragewa Al’ummar kasar tsadar kayan masarufi da ake fama dashi a kasar nan.
Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Muhammad ne ya bayyana hakan Jim kadan bayan fitowa daga ganawar majalisar tattalin arzikin jiya Alhamis karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a fadar Aso Rock dake Abuja.
Ya ce ‘mataimakin shugaban kasar ya baiwa hukumar ta NEMA umarnin gaggauta fitar da hatsin tare da hada gwiwa da jihohi a yayin rabon.
Da yake bayyana damuwar sa game da tsadar kayan masarufi, gwamna Bala Abdulkadir ya ce ‘batun abinci ba abu ne da za’a yi wasa da shi ba, a don haka ne ma ya sanya majalisar daukar wannan mataki, baya ga fitar da karin wasu tsare tsare da zasu taimaka a sauran bangarori na walwala da cigaban al’umma’.
Rahoton: Mukhtar Ahmad Birnin Kudu
You must be logged in to post a comment Login