Labarai
Jami’an Fasakauri sun kama alburusai 975 a cikin shinkafa
Jami’an Kwastam sun kama albarusai 975 da aka boye cikin buhanan shinkafa da aka yi fasa-kwauri zuwa Najeriya daga kasar waje.
Jami’an da ke aiki a Jihar Ogun ne suka kama wadannan albarusai a buhuhunan shinkafa biyar kan hanyar Palace/Ayetoro a Karamar Hukumar Imeko Afon.
Kwanturolan Kwastam na yankin, Ahmadu Shuaibu, ya ce sun kama makaman ne bayan masu fasa-kwaurinsu sun yi kokarin wucewa da su ta barauniyar hanya.
Ya kara da cewa bayan samun bayanan sirri kan ayyukan masu fasa-kwaurin makamai zuwa Najeriya ne a ranar Litinin suka kama albarusan.
A cewarsa, ana ci gaba da bincike domin kamo masu hannu wajen fasa-kwaurin makaman domin su fuskanci hukunci.
Jami’in ya bayyana fasa-kwaurin makamai a matsayin babban hadari da ke taimaka wa ayyukan ta’addanci da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya.
You must be logged in to post a comment Login