Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce duk Wanda aka kama Yana cin zarafin malaman Daji zai Kwashe shekaru 10 a gidan Yari.

Haka zalika gwamnatin ta ce za ta samar da doka ta musamman da za ta rinka Kare ganduje Daji da Dabbobin dake rayuwa a Dajin Falgore dake jihar.

Shugaban hukumar lura da gidan Ajiya da Adana namun Daji ta Kano, wato Zoo, Kwanzabeta Sadik Kura Muhammad ne ya bayyana hakan a wani bangare na bikin ranar malaman dake Lura da Dazuka ta Duniya da ya gudana a Dajin na Falgore.

Sadik Kura ta cikin wata sanarwa da Jami’ar hurda da Jama’a ta hukumar gidan Adana Namun Daji da Gandun Daji ta jihar Kano Hajiya Hauwa Adam ta fitar ya ce zai samar da ayyukan yi ga mutanan dake rayuwa a Kananan hukumomin Doguwa da Tudunwada da Kuma Sumaila Wanda suke rayuwa a kusa da Dajin na Falgore da hakan zai saka su Kara Lura da Dajin.

Ya Kuma roki al’ummomin yankin da kada su bari Dajin ya lalace su Kuma ci gaba da Lura da shi.

Ta cikin sanarwar shugaban gidan Zoo din na Kano Sadik Kura Muhammad ya Kuma godewa hukumomin dake taimakawa wajen inganta gandun Daji da Kula da tsirrai a nan Kano Irin na su ACReSAL da dai sauran su.

Ya Kuma ce a shekara Mai zuwa gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ne zai jagoranci Taron da Kansa duba da muhimmancin da yake dashi.

Anasa jawabin Daraktan dake Lura da tsare-tsaren gidan Ajiyar Namun Daji na Kano, Alhaji Ahmad Tijjani ya ce Malaman Daji suna amfani wajen Inganta rayuwar Dan Adam domin ta hanyar Kula dacgandun Daji da suke ne Mutane suke samun Ingantacciyar Iskar da suke shaka, tare da magance dumamar yanayi.

Ya Kuma ce ta hanyar aikin da suke yi suna samar da ayyukanyi ga dumbin Jama’a.

Da yake jawabi hakimin karamar hukumar Doguwa da Alhaji Zakari Iliyasu Dagacin Tagwaye ya wakilta Cewa ya yi za su bada hadin Kai wajen tabbatar da Dajin ya ci gaba da Inganta.

 

Datake jawabi Daraktar dake Lura da gidan Adana namun Daji ta Zoo Hajiya Hafsat Bello Adam Cewa ta yi za su ci gaba da baiwa mutanan dake Lura da gandun Dajin Kano kariya.

Inda tace bincike ya nuna cewa Mutane 140 daga kasashe 37 sun rasa ransu a bana wajen Lura da gandun Daji amma duk da haka baisa wasunsu sun sare da aikin ba.

Sanarwar ta Kuma ce yayin Taron an Karrama wasu daga cikin mutanan da suka rasa ransu a lokacin aiki, inda aka Mika karramawar ga iyalansu da Yan uwansu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!