Ƙetare
Shugabannin ƙasashen duniya na ci gaba da miƙa saƙon ta’aziyyar mutuwar Raila Odinga

Shugabannin ƙasashen duniya na ci gaba da miƙa saƙon ta’aziyyar mutuwar tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga wanda ya rasu a ranar Laraba, suna mai bayyana shi a matsayin uba da ya bar giɓi mai girman gaske ga dimokuradiyya a ƙasarsa.
Shugabannin Afirka da suka hada da Bola Ahmed Tinubu na Najeriya da firaministan Habasha Abiy Ahmed da shugabar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan da na Zambia Hakainde Hichilema, a sakonnin ta’aziyyar su, sun bayyana Odinga, a matsayin ɗan gwagwarmaya kuma ɗan kishin ƙasa da samun irinsa a wannan lokaci zai yi wuyar gaske.
Firaministan India Narendra Modi, ya bayyana kaɗuwarsa da mutuwar fitaccen ɗan siyasar na Kenya, har ma ya taɓo irin alaƙar da suka yi a sakon ta’aziyyarsa.
Yayin da ƙasashen Birtaniya da Faransa da Jamus suka aike da sakon ta’aziyyar su, suna bayyana marigayin a matsayin ɗan gwagwarmaya.
Odinga ya fara yin fice ne a shekarun 1980 a matsayin mai fafutukar siyasa da ke yaƙi da mulkin jam’iyya ɗaya ta shugaba Daniel Arap Moi.
An tsare Odinga daga 1982 zuwa 1988 da kuma daga 1989 zuwa 1991, ya tsere daga ƙasar bayan an sako shi a watan Yunin waccan shekarar a cikin fargabar yunkurin yi masa kisan gilla.
Odinga ya yi neman shugabancin ƙasar na farko a babban zaɓen 1997, kuma na ƙarshe shi ne a 2022, lokacin da tsohon shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta ya mara masa baya a fafatawar da ya yi da William Ruto.
You must be logged in to post a comment Login