Labarai
Gwamnatin Kano ta musanta yin watsi da Murtala Muhammed Library

Gwamnatin Jihar Kano, ta musanta zargin cewa ta yi watsi da daƙin karatu na Murtala Muhammed Library bayan wani bidiyo da matashin ɗan gwagwarmayar nan Kwamared Sadeeq Sabiʼu ya yi, da ya yadu a kafafen sada zumunta wanda ya nuna wajen na cikin mawuyacin hali.
Hakan na cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa ba a yi watsi da dakin Karatun ba, hasalima ana ci gaba da aikin gyare-gyare da sabunta shi domin mayar da shi cibiyar karatu da bincike ta zamani.
Gwamnatin ta ce, tuni ta bai wa kamfanin Global Firm Limited kwangilar gudanar da aikin.
A cewar gwamnatin jihar, an kwashe kujeru da akwatunan littattafai da sauran kayayyaki daga saman ginin zuwa ƙasa domin bai wa ’yan kwangilar damar gudanar da aikin, lamarin da ya haifar da yanayin da aka gani a bidiyon da ya tayar da ce-ce-ku-ce.
Gwamnatin ta ce ta gano cewa ɗan kwangilar ya dakatar da aikin ba tare da kammala shi ba, kuma za a ɗauki hukunci a kai, tare da tabbatar da ci gaba da aikin har sai an kammala sabinta laburaren ya dawo daidai da zamani.
You must be logged in to post a comment Login