Connect with us

Labarai

Gwamna Adeleke ya sauke Sarki bayan kotun Amurka ta same shi da aikata damfara

Published

on

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke, ya sauke Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede, bayan wata kotu a ƙasar Amurka ta same shi da laifukan damfara ta haraji da kuma halasta kudaden haram.

 

Matakin ya biyo bayan samun sahihin kwafin hukuncin kotun Ohio da gwamnatin ta Osun ta yi.

 

Mai magana da yawun gwamnan, Olawale Rasheed, ya ce, gwamnatin jihar ta Osun, ta ɗauki matakin ne domin kare martabar masarautar da tabbatar da zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci. 

 

Tun a watan Agustan 2025 ne kotun tarayya ta Ohio ta yankewa sarkin hukuncin daurin watanni 56 bisa laifukan damfara da kuma ƙarya wajen biyan haraji. Gwamnatin Osun ta bayyana fara shirye-shiryen naɗa sabon sarki a nan gaba kadan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!