Labarai
Gwamnatin Jigawa ta kashe fiye da biliyan 300 wajen gina hanyoyi da wasu ayyuka

Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe sama da Naira biliyan 300 wajen ginin hanyoyi da sauran ayyukan more rayuwa cikin shekaru 2.
Babban daraktan hukumar tabbatar da bin ka’idojin Kwangila da bibiyar aiyuka Kasim Muhammad ne ya bayyana a gurin rufe wani taro da aka gudanar a garin Gumel.
A cewar daraktan gwamnatin jihar ta bada Kwangilar sabin hanyoyi 46 wadda ya kai kilomita 976 a shekarar da ta gabata, tare da karasa aiyukan da aka gada daga gwamnatin baya.
Haka nan ya kara da cewa saukaka zirga-zirga da bunkasa noma da safarar kayayyaki daga wani bangaren zuwa wani ma daga cikin manufar yin aiyukan.
Kazalika ya ce gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Malam Umar Namadi ta bayar da wasu aiyukan masu yawa a bangaren Lafiya da Ilimi da kuma Noma don inganta rayuwa da kuma walwalar al’ummar jihar.
You must be logged in to post a comment Login