Labarai
Ɗan gidan Aminu Abdussalamu ya yi karar Sunusi bature

Dan gidan tsohon mataimakin gwamna Kwamared Aminu Abdussalamu Gwarzo, Alhaji Mujahid Aminu Abdussalamu Gwarzo, ya yi karar Daraktan yada labaran gwamnan Kano Sunusi bature Dawakin Tofa a ofishin kwamishinan Yan Sanda bisa zarginsa da yi wa tsohon mataimakin gwamnan kazafi.
Lauyan dan gidan tsohon mataimakin gwamnan Barista Nazifi Mustapha Goron Dutse ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio bayan da ya shigar da ƙarar ta cikin takardar da ya kai ofishin kwamishinan a yau Laraba.
Ya ce, sun yi karar Sunusi bature Dawakin Tofa, ne bisa zarginsa da yi wa Kwamared Aminu Abdussalamu Gwarzo, kazafin cewa ya na karbar kudade daga kananan hukumomin jihar Kano 44 lokacin da ya ke da mukamin kwamishina.
You must be logged in to post a comment Login