Connect with us

Labarai

INEC ta bayyana jam’iyyu 3 a matsayin wanda za su fafata a zaɓen Dawakin Kudu da Warawa

Published

on

Hukumar zabe ta kasa INEC ta ce Jam’iyyu uku ne zasu fafata a zaben cike gurbi da za a gudanar na dan majalisar tarayya a kananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa a ranar Asabar mai zuwa.

Shugaban hukumar a nan Kano Ambassador Abdu A. Zango ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala tattaunawa da jami’an tsaro kan yadda zaben zai kasan ce.

A cewar sa Jam’iyyun da zasu fafata a zaben sun hadar da APC da APM sai kuma LP wato Labor Party.

Da ya ke jawabi kwamishinan yan sandan Kano Ibrahim Adamu Bakori ta bakin mataimakinsa kan ayyuka na musamman DCP Lawan Isah Mani ya ce, sun shirya tsaf dan bayar da tsaro a lokacin zaben, kuma zasu sanya dokar hana zirga-zirgar ababen hawa a yankunan da za a yi zabukan.

Jami’an tsaro da dama ne dai suka halarci tattaunawar dangane da yadda za a bayar da tsaro a lokacin zaben cike gurbin da za a gudanar a kananan hukumomin na Dawakin Kudu da Warawa a ranar Asabar mai zuwa 20 ga watan Yunin da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!