Labarai
Shugaba Tinubu ya umarci ƴan wasan Najeriya su kasance jakadu nagari

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya umarci ƴan wasan da za su wakilci Najeriya a gasar wasannin Commonwealth ta 2026 da za a gudanar a birnin Glasgow na ƙasar Scotland, da su fafata cikin mutunci da ladabi.
Shugaba Tinubu, ya bayyana hakan ne yayin da ya ke bankwana da tawagar yan wasan a wani biki da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Aso Rock Villa.
Haka kuma, ya buƙace su da su kasance masu ƙwazo tare da zama jakadun Najeriya nagari.
You must be logged in to post a comment Login