Labarai
Shugaba Tinubu ya bukaci yan wasan Najeriya da su kare martabar kasar nan

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci ‘yan wasan Najeriya da ke shirin halartar gasar World Athletics Relays a ƙasar Botswana da su nuna ƙwazo da jajircewa domin ɗaga tutar ƙasa.
Daraktan Janar na Hukumar Wasanni ta Ƙasa, Bukola Olopade, ne ya isar da wannan saƙo a yayin da yake ganawa da ‘yan wasan bayan kammala atisayensu na ƙarshe a birnin Gaborone.
Olopade ya bayyana cewa gasar na da matuƙar muhimmanci, kasancewar tana zama wata hanya ta samun gurbin shiga manyan gasannin duniya, yana mai cewa wasan motsa jiki na daga cikin fannoni da suka fi bai wa Najeriya ɗaukaka a idon duniya.
Ya kuma buƙaci ‘yan wasan da su fafata ba kawai domin kansu ba, har ma domin ƙasa, jihohinsu da kuma Shugaban ƙasa, yana mai cewa Najeriya na sa ran dawowarsu da nasara.
Haka kuma, ya isar da fatan alheri daga Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa, Shehu Dikko, ga ‘yan wasan gabanin fara gasar.
Rahotanni sun nuna cewa Najeriya na cikin ƙasashen da za su fafata a dukkan nau’ikan gasar relay guda shida, yayin da ƙasar ta taba lashe lambar zinariya a 2015 da kuma tagulla a 2014 a irin wannan gasa.
You must be logged in to post a comment Login