Labarai
Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudurin ta na cigaba da inganta harkokin kiwon lafiya a fadin Jihar.
Kwamishinan lafiya na Jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da wasu ayyuka biyu da suka hada da raba kayan aiki a babban asbitin garin Gwarzo tare da bude wata akarantar Islamiyya.
Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya kara da cewa Gwamnatin Kano ta siyo kayayyakin aiki na Asbitin da kudin sa ya kai Naira Millyan 70, don inganta harkokin kiwon lafiya a yankin.
Da yake bayani dangane da cutar kwalara da ta barke a jihar Kano,Kwamishinan yace Jihohi biyar ne Arewacin Kasarnan suka kamu da wannan cuta amma kawo yanzu gwamnatin ta dauki matakan gaggawa don magancesu.
Kwamishinan yayi kira ga al’umma dasu kula da tsafatar abinci da kuma mahllin su don gujewa barkewar cututuka.
A dai makwan da ya gabata ne muka kawo muku rahoto kan barkewar cutar kwalara a kananan hukumomin Gwarzo da Bebeji, yayin da aka sami rahoton mutuwar mutum 9 a karamar hukumar Gwarzo sai kuma mutum 10 a karamar hukumar Bebeji.